in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira da a kara kaimi wajen samar da makamashi mai dorewa
2014-06-06 14:21:16 cri

Wasu manyan jami'an MDD sun bayyana cewar, samar da makamashi yana da mahimmancin gaske, a wajen kawar da talauci da kuma magance matsalar canjin yanayi, sun kuma yi kira da a mai da hankali wajen saka jari, domin a kawo canjin ga tsarin makamashi na duniya.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon, a yayin da yake jawabi ga wani taron farko na shekara-shekara a kan samar da makamashi mai dorewa, ya ce, makamashi mai dorewa wani abu ne, da zai iya kawar da talauci tare da samar da habbakar tattalin arziki na bai daya, da kuma lafiyayyen yanayi.

Wannan taron na da niyyar kara janyo hankalin jama'a, a game da wani kokarin da aka yi na shekara 2011, wanda kasashe da yawa da kungiyoyin kare hakkin bil'adama da na tattalin arziki suka halarta, da zimmar samar da makamashi mai dorewa ga kowa da kowa nan da shekara ta 2030.

A wurin taron a jiya Alhamis, babban sakataren MDD da kuma shugaban babban bankin duniya Jim Yong Kim, da kuma shugaban babban taro na MDD John Ashe, sun kaddamar da shekaru goma na MDD na samar da makamashi mai dorewa ga dukanin duniya daga shekara ta 2014, zuwa shekara ta 2024.

Ban, ya bayyana cewar, shekaru goma na samar da makamashi mai dorewa za su sa duniya ta kara kusanta ga muradinta na samar da makamashi na duniya baki daya, da kuma samar da kyakkyawar rayuwa, da falala ga daukacin jama'a. Kamar yadda ya ce, shekaru biyu na farko daga cikin shekaru 10, da aka kebe, za'a mai da hankali ne a kan wayar da kan jama'a a kan samar da makamashi a bangaren lafiyar mata da yara.

A nasa jawabin, John Ashe ya ce, tarihin habbakar al'ummar zamani, wani abu ne da ke tafiya tare da ci gaban makamashi, da kuma tasirin shi a kan jama'a, tattalin arziki da yanayi

Ya kara da cewar, makamashi ya shiga rayuwar dan'adam a dukanin matakai na rayuwarsa, saboda haka dukanin al'ummomi na kasashen duniya suna bukatar makamashi, domin ci gabansu da kuma samu bunkasuwa. Wannan kuma kamar yadda ya ce, shi ne dalilin da ya sa ya kamata yanzu a magance wannan matsalar ta rashin samar da makamashi mai dorewa, saboda mahimmancin lamarin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China