A yayin da yake jawabin a wajen bikin ranar iyalai ta duniya, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi nuni da gagarumar rawar da rukuni na iyali ke takawa domin samun nasarar cimma manufofin duniya da aka amince da su, wadanda za su samar da duniya ta gari ga dokacin bil'adama.
Bikin zagayowar ranar na wannan shekarar ya zo daidai da zagayowar shekaru 20 din da aka yi ana bikin wannan rana ta iyalai, wacce kuma ta samar da wata dama ta kara mai da hankali a kan rawar da iyalai ke takawa a ci gaba, musammamn wajen cimma manufofin ci gaba na duniya wadanda aka amince da su.
Ban, ya yi kira da a hada kawunan iyalan duniya ta hanyar gangami, a yayin da kasashen ke kara kaimi wajen samar da makoma mai dorewa, tare kuma da samun nasara ta kawar da talauci, a karkashin shirin kaiwa ga cimma manufofin ci gaba na wannan karni MDGS, wanda zai samar da sabon tsarin ci gaba, tare kuma da magance matsalar dumamar yanayi. (Suwaiba)