in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD zai karfafa tallafi game da harkokin tsaro
2014-04-29 10:06:27 cri

Kwamitin tsaron MDD ya amince da wani kuduri, da ya tanaji baiwa kasashen da suke farfadowa daga rigingimu karin tallafi a fannonin tsaro, ta hanyar gudanar da kwaskwarima ga manufofin tsaronsu.

Sabon kudurin ya kuma tanaji baiwa irin wadannan kasashe taimako, na magance matsalolin da suka iya fuskanta, yayin da suke tsara manufofin ci gabansu. Matakin da aka yi imanin cewa, zai ba da cikakkiyar damar wanzar da zaman lafiya da lumana, da yaki da fatara, tare da maido da doka da oda a irin wadannan kasashe.

Kaza lika hakan zai taimaka matuka wajen samar da ingantacciyar gwamnati, da kuma kare kasashen da rikici ya daidaita sake komawa gidan jiya.

Wannan dai kuduri da daukacin wakilan kwamitin 15 suka amince da shi a zaman da ya gudana ranar Litinin, shi ne irin sa na farko, da zai baiwa sashen aiwatar da kwaskwarima ga harkokin tsaron irin wadancan kasashe tallafi kai tsaye daga kwamitin tsaron majalissar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China