Shugabannin kasashen gabashin Afrika za su yi zaman taro a Addis Abeba na kasar Habasha domin kokarin karfafa shirin zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu da kuma cimma wata mafitar siyasa kan rikicin da kasar take fama da shi tun yau da kusan watanni shida.
Wadannan shawarwarin a karkashin shiga tsakanin kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka ta IGAD, a matsayin babbar kungiyar kasashen gabashin Afrika, an fara su a ranar Litinin.
Tarurukan ministocin kungiyar IGAD da na shugabanni da gwamnatocin wannan kungiya za su gudana a ranar yau goma ga wata, in ji sakataren kungiyar IGAD a cikin wata sanarwa.
Rikicin Sudan ta Kudu ya barke a Juba, babban birnin kasar a tsakiyar watan Disamban shekarar 2013, sannan ya bazu zuwa wasu yankunan kasar. (Maman Ada)