in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 78 suka mutu a cikin wasu hare-hare a Peshawar na Pakistan
2013-09-23 15:34:54 cri

Akalla mutane 78 suka kwanta dama a yayin da wasu sama da 120 suka ji rauni a ranar Lahadi a cikin wasu hare-haren bama bamai na kunar bakin wake a kan wata mujami'a a birnin Peshawar dake arewa maso yammacin kasar Paskistan, a cewar majiyoyin asibiti. Mataimakin kwamishinan 'yan sandar Peshawar Zaheer-ul-Islam ya tabbatar da wannan adadi, tare da bayyana cewa, an isar da wadanda suka jikkata a asibitin 'Lady Reading' dake birnin domin samun kulawa. A cewar jami'in, hadarin ya abku ne da misalin karfe 11 da mintoci 45 da safe, agogon wurin, 'yan kunar bakin waken sun tada nakiyoyin dake daure a jikinsu a cikin ginin na ibada, a yayin masu ibada 500 zuwa 600 suke kokarin fitowa bayan sun kammala ibadarsu.

Haka kuma jami'in ya jaddada cewa, mujami'ar da aka kai mata hari a Peshawar, hedkwatar jihar Khyber Pakhtoonkhwa tana da dogon tarihi.

A nasa bangare, babban darektan asibitin 'Lady Reading' ya bayyana cewa, 'yan sanda 2, kananan yara 7 da mata 34 suna cikin mutanen da suka mutu, sannan kuma mata 44 da kananan yara 11 suna cikin wadanda suka ji rauni. Sufeto janar na jami'an lalata nakiyoyi, mista Shafqat Malik ya bayyana cewa, boma boman sun tashe daya bayan daya, kowanen 'yan kunar bakin baken biyu na dauke da bam akalla kilogram 7.

Har yanzu babu wata kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai wadannan tagwayen hare-hare, amma tuni shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain da faraministan kasar Nawaz Sharif suka yi allawadai da hare-haren. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China