in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe baki 'yan yawon bude ido 10 a arewacin Pakistan
2013-06-24 10:18:08 cri

Ministan harkokin cikin gida na kasar Pakistan Chaudhry Nisar Ali Khan, ya ce, wasu mahara sun kashe baki 'yan yawon bude ido guda 10 a wani harin da aka kai yankin arewacin Gilgit-Baltistan da ke Pakistan a ranar Lahadi.

Ministan ya ce, rahotannin farko sun nuna cewa, 'yan kasashen waje guda 9 da 'yan kasar Pakistan 2 ne aka kashe a harin, amma daga bisani, an tabbatar da cewa, daya daga cikin wanda ake zaton 'dan kasar Pakistan ne, 'dan kasar Nepal ne.

Ministan ya kuma bayyana cewa, an gano asalin saura hudu daga cikin 'yan kasashen wajen da aka kashen, wadanda suka hada da Sinawa biyu, Ba'amurka 'dan asalin kasar Sin, da kuma 'dan kasar Nepal guda. Sai dai har yanzu ba a gano asalin sauran mutane guda 6 ba.

Tun da farko dai, ofishin jakadancin kasar Sin, ya bukaci sassan kasar Pakistan da abin ya shafa, da su yi dukkan kokarin da ya dace na ceto Sinawan da suka ji rauni tare da tabbatar da kare lafiyar dukkan Sinawan da ke kasar.

Jim kadan bayan faruwar wannan hari, firaminista da kuma shugaban kasar ta Pakistan Asif Ali Zardari, dukkansu sun bayyana kaduwa da kuma yin Allah-wadai da wannan mummunan hari da mayakan Jundallah, reshen kungiyar Taliban na Pakistan suka dauki alhakin kaiwa.

Dakarun tsaron Pakistan sun killace dukkan hanyoyin da suka kai ga wurin da aka kai harin a kokarin farautar maharan, sai dai har yanzu babu wani karin bayani. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China