An kame wani mutum mai hallaka jama'a wanda da ma tun asali aka kafa tarkon kama shi, a sabili da dadewar da ya yi, yana addabar jama'ar jihar Ogun, kudu maso yammacin Nijeriya, kuma a yanzu haka ta cimma ruwa, domin mutumin yana hannun 'yan sanda.
A yayin wani taron manema labarai a jiya Laraba, kakakin jami'an 'yan sandar jihar Ogun, Muyiwa Adejobi, ya ce, wanda aka kaman, wanda kuma aka asirta sunansa, an kama shi ne, a wani kauye da ake kira Iyana Egbado, dake cikin karamar hukumar Ewekero dake jihar ta Ogun a safiyar Laraba, kuma kamar yadda jami'in ya ce, an kama wanda ake zargi ne da naman bil'adama.
Kakakin 'yan sandan Adejobi wanda ya yi jawabi a garin Abeokuta, hedkwatar jihar ta Ogun ya ce, mazauna kauyen su ne suka tuntubi jami'an tsaro, wadanda kuma nan take suka shiga aiki, kamar yadda kakakin ya ce, a halin yanzu an fara gudanar da bincike a kan lamarin, musamman domin a gano ta hanyar bincike na gwaji da ilmin fasaha, gaskiyar asalin naman da aka kama wanda ake zargi da shi, shin naman na mutum ne ko kuma a'a. Kakakin ya ce, jawabi dake fita daga bakin wanda aka kama soki burutsu ne kawai, kuma yana yin halayya kamar mahaukaci, to amma 'yan sanda sun lashi takobin gano gaskiyar wannan aika-aika. (Suwaiba)