in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ba ta da burin aiwatar da manufofin fito-na-fito
2014-05-06 09:48:35 cri

Mahukunta a Zimbabwe sun bayyana aniyar kasar wajen inganta manufofinta, ta yadda za su dace da bukatun masu burin zuba jari daga kasashen ketare.

A cewar ministan kudin kasar Patrick Chinamasa, kasarsa ba ta da niyyar daukar matakan fito-na-fito da ka iya gallazawa masu fatan zuba jari. Chinamasa wanda ya bayyana hakan ga mahalarta taron masu ruwa da tsaki a fannin masana'antu, da aka gudanar a birnin Harare, ya kara da cewa, Zimbabwe na fatan kulla abota da sabbi, tare da karfafa huldar dake wanzuwa tsakanin ta da dadaddun kawayen ta.

Daga nan sai ya nanata manufar kasar ta kokarin samun bunkasuwa, da cin moriyar kawancen tattalin arziki, da cinikayya tare da sauran kasashen duniya, matakin da ya ce, kasar na burin aiwatarwa ba tare da gindaya wasu sharudda ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China