in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ba za ta mai da rand matsayin kudin kasar daya tak ba
2014-05-07 12:18:35 cri

Babban bankin Zimbabwe ya ce, zai ci gaba da amfani da kudade daban daban a kasar, a inda kuma bankin ya ce, ba zai mai da kudin rand, na kasar Afrika ta Kudun a matsayin kudin da kasar daya tak ba.

A yayin da yake jawabi lokacin taron kwanaki biyu na duniya, a game da taimakawa Zimbabwe kara shiga cikin jerin kasashen duniya, mataimakin gwamnan babban bankin Zimbabwe Khupukile Mlambo ya yi watsi da shawarar da wasu wadanda suka gabatar da kasidu suka bayar, a kan Zimbabwe ta dinga amfani da kudin rand na Afrika ta Kudu. Mlambo ya ce, ba zai yiwu Zimbabwe ta yi amfani da rand na Afrika ta Kudu ba saboda rand din yana tangal-tangal.

Wani malamin jami'ar zimbabwe mai koyar darasin tattalin arziki, a jami'ar Zimbabwe ya taba ba da shawara cewar, tun da Afrika ta Kudu babbar abokiyar cinikin Zimbabwe ce, ya kamata Zimbabwe ta shiga cikin rukunin kasashe masu amfani da kudin rand domin a inganta halin tattalin arzikin kasar ta Zimbabwe. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China