A jiya Litinin ne shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu, ya rantsar da sabon mataimakinsa Cyril Ramaphosa, yayin bikin kaddamar da sabuwar majalissar zartaswar kasar da aka yi a fadar gwamnati dake birnin Pretoria.
Bayan rantsar da sabon mataimakin shugaban kasar ne kuma, babban mai shari'ar kasar Mogoeng Mogoeng, ya rantsar da ministocin majalissar zartaswar da shugaba Zuma ya nada a ranar Lahadi.
Nadin ministocin 35 dai ya kasance matakin karshe na kafuwar sabuwar gwamnatin kasar, biyowa bayan babban zaben da ya gabata a ranar 7 ga watan nan.
Sabuwar gwamnatin dai ta kunshi sabbin ma'aikatu, da kuma wasu da aka yiwa gyaran fuska, matakin da shugaba Zuman ya ce zai taimaka wajen cimma kudurorin da gwamnatinsa za ta sanya gaba. (Saminu)