Babban sifeton rundunar 'yan sandan tarayyar Najeriya Mohammed Abubakar, ya ce, gwamnati na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, don ganin an kawo karshen hare-haren ta'addanci da ke wakana a sassan kasar.
Abubakar ya bayyana hakan ne a garin Jos, babban birnin jihar Plateau, yayin ziyarar jaje da ya kai wuraren da wasu bama-bamai suka tashi, da kuma asibitocin da aka kwantar da wadanda suka jikkata.
Babban sifeton 'yan sandan ya bayyana harin bama-baman na ranar Talata, a matsayin wani mummunan aikin rashin tausayi.
Daga nan sai ya mika sakon jajen shugaba Goodluck Jonathan na Najeriyar ga al'ummar jihar ta Plateau, yana mai cewa, fadar gwamnatin kasar, ta lashi takobin kakkabe ayyukan ta'addanci daga daukacin sassan kasar baki daya. (Saminu)