Kasar Rwanda za ta dauki bakuncin wani dandali wanda za'a yi a babban birnin kasar Kigali, a kan fitar da kayayyaki kasashen waje.
Jami'an gudanar da dandali a kan bunkasa kayayyakin da ake fitarwa ketare, sun ce, wannan dandali zai taimakawa manya da kananan kamfanoni, samun wata dama ta cudanya da kasuwanni na duniya kai tsaye.
Shi dai wannan taron duniya na bunkasa kayayyakin da ake fitarwa kasashen ketare wanda ake yin shi kowace shekara. Cibiyar cinikayya ta duniya da kuma hukumar hadin gwiwar taron cinikayya da ci gaba na MDD da kuma kungiyar kasuwanci ta duniya su ne za su gudanar da taron na Rwanda tun daga ranar 16 zuwa 17, ga watan Satumbar wannan shekarar. Wannan shi ne karo na farko da ake gudanar da irin wannan taro a Afrika.
Ana sa ran mutane fiye da 400 za su halarci taron, cikin wadanda za su halarci taron, akwai masu tsara dokoki da 'yan kasuwa, da kuma shugabannin hukumomi dake goyon bayan kasuwanci da kuma kungiyoyi na duniya daga sassa dabam-dabam na duniya. (Suwaiba)