Tsohon hafsan soja, kuma 'dan takaran shugaban kasa a yanzu haka a kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi a ranar Litinin din nan 5 ga wata ya sanar da cewa, babu wata makoma ga kungiyar 'yan uwa musulmi idan har ya samu nasarar zaben shugaban kasar mai zuwa.
Al-Sisi, lokacin da yake amsa tambayar ko zaben shi na nufin karshen kungiyar, ya mai da amsar cewa, babu wani suna kamar kungiyar 'yan uwa musulmi da zai sake kunno kai a karkashin mulkinsa. Wannan furucin na al-Sisi ya nuna cewa, mahukuntan kasar karkashin goyon bayan sojoji na dakile ta, ganin yadda daman kungiyar take ta samun hari mai tsanani tun watan Yulin da ya gabata.
Kungiyar ta 'yan uwa musulmi wato Muslim Brotherhood wadda hambararren shugaban kasar Mohamed Morsi yake karkashin ta, a yanzu haka an zayyana sunan ta a cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.
Mohamed Morsi dai, sojojin al-Sisi ne suka hambarar da shi a watan Yulin bara sakamakon zanga-zangar gama gari da jama'a suka yi ta yi dangane da gwamnatin sa ta shekara daya. (Fatimah)