in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar tashe-tashen hankula a CAR sun sanya al'umma cikin mawuyacin hali, in ji MDD
2014-04-08 09:35:43 cri

Rahotannin baya bayan nan daga ofisoshin hukumar noma ta duniya, da hukumar abinci ta WFP sun nuna cewa, halin matsin da al'ummun Afirka ta Tsakiya CAR ke ciki, ya toshe kafar agazawa juna.

Rahotannin da hukumomin biyu suka fitar, sun bayyana rikicin kasar da ya barke tun cikin watan Disambar shekarar 2012, a matsayin babban dalilin lalacewar ababen more rayuwa, asarar kayan abinci, da ma karancin sauran kayan bukatu na yau da kullum a kasar.

Da yake karin haske don gane da hakan, kakakin MDD Farhan Haq, ya ce, tarin matsalolin da tashe-tashen hankulan kasar suka haifar, ya yi matukar gurgunta tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta.

Haq, wanda ya hakaito bayanan dake kunshe cikin rahotannin hukumomin biyu, ya ce, Afirka ta Tsakiya za ta bukaci lokaci mai tsahon gaske, kafin ta samu damar farfadowa yadda ya kamata.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya kai ziyara Afirka ta Tsakiya, a wani yunkuri na janyo hankalin duniya kan halin da kasar ke ciki, tare da fatan al'ummar kasar za su koyi darasi daga kasar Rwanda, kasar da rikicin kabilanci ya haifar da kisan kiyasi, da kawo yau ake ci gaba da jimamin aukuwarsa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China