in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana matukar damuwa ga tabarbarewar yanayi a CAR
2014-04-02 10:45:08 cri

Manyan jami'an MDD na ci gaba da bayyana matukar damuwa, ga mawuyacin halin da fararen hula ke ciki a janhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR, ciki hadda batun karuwar zub da jini a babban birnin kasar Bangui.

Da take tofa albarkacin bakin ta don gane da hakan, kakakin hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD Cecile Pouilly, ta ce, tashe-tashen hankulan da suka auku daga ranar 22 ga watan Maris kawo yanzu, sun hallaka mutane 60. Don haka ta yi kira ga kasashen duniya, da su amsa kiran babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, na samar da karin dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar, don samar da kariya ga rayukan fararen hula.

Ita kuwa a nata jawabi, kakakin hukumar lura da 'yan gudun hijirar majalissar Fatoumata Lejeune-Kaba, bayyana damuwa ta yi, da yadda rikicin kabilanci a kasar, ya tilasawa dubban al'umma kauracewa gidajen su. Lejeune-Kaba, ta ce, yanzu haka al'ummar musulmi kimanin 20,000 ne ke zaman dar dar, a yankunan da ke karkashin ikon 'yan kungiyar sa kai ta Anti-Balaka.

A cewar ta, ofishin MDD na UNHCR, na da burin taimakawa wadannan mutane wajen sauya musu matsuguni a ciki da wajen kasar. Baya ga shirin tura wakilai, da za su tabbatar da kare hakkokin bil'Adama, da tabbatar da isar kayayyakin agaji zuwa yankuna, musamman wadanda al'ummun su suka fi fuskantar barazana. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China