Hukumomin ayyukan jin kai na MDD da abokan huldarsu sun yi kira a ranar Laraba cewa, suna bukatar dalar Amurka miliyan 274 domin taimakawa mutanen dake gujewa rikici a kasar Afrika ta Tsakiya (CAR) tun daga watan Disamban da ya gabata.
Hukumomin MDD goma sha hudu, wadanda a ciki akwai hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (HCR), kungiyar noma da abinci ta MDD (FAO), asusun MDD kan al'umma (FNUAP), asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF), kungiyar abinci ta duniya (PAM) da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (OMS) da sauran kungiyoyi masu zaman kansu sun bukaci a ranar Laraba masu hannu da shuni da su zuba kudi domin gudanar da ayyukan ba da agajin gaggawa ga fararen hula dake ficewa daga kasar tun cikin watan Disamban shekarar 2013, in ji kakakin MDD Stephane Dujarrac a yayin wani taron manema labarai.
Hukumomin na neman dalar Amurka miliyan 274 domin shirin shiyya na taimako ga kasar Afrika ta Tsakiya, ta yadda za'a samar da kudaden wadannan ayyuka a wannan shekara, in ji mista Dujarrac.
Jami'in ya cigaba da cewa, gamayyar ba da agaji ta nuna cewa, mutanen da suka fice daga CAR za su kai dubu 367 da 200 a karshen shekarar 2014, domin haka ne take neman wannan kudi bisa shirin shiyya na taimako.
Dukkan hukumominmu dake aiki a wannan shiyya suna fama da rashin kudin gudanar da ayyukansu, in ji babban jami'in kungiyar HCR Antonio Guterres a lokacin gabatar da shirin shiyya na taimako a birnin Geneva. (Maman Ada)