Kasar Amurka ta aika sojoji zuwa kasar Chadi, a kokarin da kasashe suke yi na gano 'yan matan Chibok su fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka sace a Nigeriya.
A cikin wasikar da ya aike wa majalisar dokokin Amirka, shugaba Barack Obama ya ce, sojojin Amurkan su kimanin tamanin, za su taimaka wajen tattara bayanai na sirri, da sa-ido, da kuma yin shawagi da jiragen leken asiri a arewacin Najeriya, da kuma yankunan da ke zagayen arewacin Nigeriyar.
Obama ya ce, rundunar dakarun Amurka za ta ci gaba da kasancewa a makwabciyar kasa ta Chadi, har sai an kai wani mataki da ba za a bukaci goyon bayan Chadin ba a wajen warware matsalar sace 'yan matan na Chibok. (Suwaiba)