Akalla mutane 15 suka mutu, kana kusan 30 suka jikkata a ranar Lahadi a Kinshasa, a yayin wata gasar kwallon kafa da ta hada kungiyar V.Club ta Kinshasa da kungiyar TP Mazembe ta Lubumbashi a filin wasan Tata Raphael.
Wannan adadi, an bayar da shi a ranar Lahadi da yamma a cikin wata sanarwar da ofishin ministan cikin gidan DRC-Congo ya gabatar a gidan talabijin na kasa.
Amma wata majiya mai tushe daga kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Congo ta tabbatar da cewa, wannan adadi zai iyar haura haka.
Ga duk alamu, wannan adadi zai karu. Ina iyar cimma fiye da mutuwar mutane 20 da kusan dari wadanda suka jikkata, in ji kungiyar agaji ta Red Cross. (Maman Ada)




