in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun sace 'yan mata a Najeriya ya mamaye ranar yara
2014-05-29 10:17:55 cri

A ranar Talatar da ta gabata ne aka gudanar da bikin ranar yara a tarayyar Najeriya, sai dai ba a gudanar da shagulgula kamar yadda aka sa ba, sakamakon alhinin sace 'yan matan makarantar nan ta Chibok su sama da 270.

Cikin wani jawabi da ta gabatar yayin wani taron ganawa da 'yan jaridu a birnin Abuja, minista a ma'aikatar mata da ci gaban jama'a Zainab Maina, ta ce, gwamnati na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin kaiwa ga sako yaran.

A jihar Gombe dake arewacin kasar kuwa, kwamishiniyar ma'aikatar mata ta jihar Fatima Abubakar, cewa ta yi, gwamnatin jihar ta soke gudanar da bikin a bana, domin nuna alhini ga kisan 'yan makarantar kwajejin ilimi ta Buni Yadin jihar Yobe, wanda ya faru ciki watan Fabarairu. Ta ce, maimakon hakan, an gudanar da addu'o'i na musamman, na fatan kawo karshen matsalar tsaro dake addabar kasar, da ma kaiwa ga kubutar 'yan matan da ke hannun mayakan Boko Haram.

Hakan dai na zuwa ne a gabar da gwamnatin jihar Bauchi dake arewacin kasar, ta kafa wani kwamiti na musamman, domin ba da kariya ga yara daga dukkanin wani nau'i na keta hakkinsu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China