Ministan lafiya na kasar Najeriya Onyebuchi Chukwu, ya fada a ranar Litinin cewa, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon bullar cutar kwalara a kasar da ke yammacin Afirka ya karu zuwa 74.
Ministan ya shaidawa wani taron likitoci a Abuja, babban birnin kasar cewa, kimanin mutane 373 ne suka kamu da cutar.
Bayanai na nuna cewa, a cikin makwannin da suka gabata ne, aka samu barkewar cutar a jihohin Filato, Sokoto, Zamfara da jihar Lagos.
Don haka, ministan ya bukaci 'yan Najeriya, da su rika daukar batun tsafta da muhimmancin gaske, yana mai cewa, wajibi ne. 'yan Najeriya su daina yin bayan gida a wuraren da ba su dace ba, kana su rika shan ruwa mai tsafta.
Ministan ya kuma baiwa jama'a tabbacin cewa, gwamnatin tana aiki tare da jihohin da aka samu barkewar wannan cuta a kokarin daukar matakan da suka kamata. (Ibrahim)