Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bayyana cewa, an samu nasarar shawo kan cutar kwalara da ta halaka a kalla mutane 71 a jihar.
Kwamishin lafiya na jihar Abubakar Labaran ne ya tabbatar da hakan ranar Lahadi, yana mai cewa, a halin yanzu gwamnatin jihar ta himmantu wajen ilimantar da jama'a game da muhimmancin kula da lafiyar yara 'yan kasa da shekaru 5.
A cewarsa, yanzu an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba na fara allurar riga kafin cutar shan-Inna da sauran cututtukan da ke halaka yara a jihar, kana an raba isassun magunguna a dukkan kananan hukumomi 44 da ke jihar.
Kwamishinan ya kuma jaddada bukatar da ke akwai ga iyaye, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya, da su kara kokarin da suka yi wajen ilimantar da jama'a game da muhimmancin diga wa yara 'yan kasa da shekaru 5 alluran riga kafi.
Wani jam'in cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya, ya bayyana cewa, sama da mutane 2,000 ne aka samu rahoton cewa, sun kamu da cutar a yankunan da cutar ta yadu a cikin watanni biyu da suka gabata. (Ibrahim)