A ranar Lahadi 20 ga wata ne aka rufe karbar takardun 'yan takarar zaben shugaban kasar Masar a hukunce, inda shugaban rikon kwaryar kasar Abdel Fattah Sisi, da Hamdeen Sabahi suka kasance 'yan takara biyu rak, da suka mika takardun bukatar shigar su babban zaben kasar.
An kuma sanya ranar 26 da 27 ga watan Mayun dake tafe, a matsayin ranekun gudanar da zagayen farko na zaben, wanda manazarta da dama ke hasashen Sisi ne zai samu nasarar lashe shi.
Dokar zaben kasar dai ta tanaji tattara sanya hannun mutane akalla 25,000, daga akalla lardunan kasar 15, kafin amincewa da mutum ya kasance 'dan takarar shugabancin kasar. Bisa kuma alkaluman da aka tattara, shugaba Sisi ya samu adadin sanya hannu 188,930, yayin da abokin takararsa Sabahi ke da 31,555.
Kaza lika 'yan takarar biyu na da ikon mika bukatar rashin amincewa da juna a ranekun Talata da Laraba, yayin da kuma hukumar gudanar da zaben kasar za ta fidda sunayen 'yan takarar a hukunce ranar 2 ga watan Mayu mai zuwa, a kuma fara yakin neman zabe tun daga ran 3 ga watan na Mayu.
Babban zaben kasar ta Masar dai ya biyo bayan hambarar da zababbiyar gwamnatin Mohamed Morsi, da Abdel Fattah Sisi ya yi cikin watan Yulin bara, sakamakon zanga-zangar nuna rashin amincewa da gwamnatin daga wasu sassan al'ummar kasar. (Saminu)