in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kiran tsagaita wutar rikicin Sudan ta Kudu tsawon wata guda
2014-04-30 15:21:23 cri

Babban jami'in MDD dake gudanar da ayyukan ba da agaji a kasar Sudan ta Kudu, Toby Lanzer ya yi kira ga 'yan tawaye masu fada da juna da su dakatar da tashin hankalin da suke yi a kasar har tsawon wata guda.

Babban jami'in ya ce, samar da zaman lumana na wata guda a watan Mayu, zai taimaka wajen samar da yanayi mai kariya ga mutane da suka fada cikin bala'i a sakamakon kasancewar rikicin a cikin watanni hudu da suka shude.

Jami'in ya ce, samar da tabbacin tsagaita wutar rikicin tsawon wata daya zai ba mutane damar zama cikin kariya, tare da samun damar zuwa duk inda suke muradi ba tare da wata fargabar tashin hankali ba.

Wannan sanarwar ta biyo bayan nuna takaici da MDD ta yi a game da halin da ake ciki a Sudan ta Kudu, inda rikicin siyasar da ya barke a kasar a tsakiyar watan Disambar bara tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da tsohon mataimakin shi, Riek machar ya haifar da asarar dubannin rayuka, a inda kuma rikicin ya sanya dubannin jama'a su neman mafaka a sansanonin MDD dake kasar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China