in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zuma ya bukaci AU da ta dauki matakan tabbatar da zaman lafiya mai karko a Afrika
2014-05-20 10:19:31 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya yi kira a ranar Litinin ga kungiyar tarayyar Afrika (AU) da ta dauki nagartattun matakan da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro cikin karko a nahiyar Afrika.

Mista Zuma ya yi wannan kira domin mai da martini kan sace 'yan mata fiye da 200 a Najeriya, da kuma haren baya bayan nan a kasar Kenya.

Shugaban Afrika ta Kudu ya bayyana damuwarsa kan ayyukan wasu kungiyoyi masu makamai da suka yi kaka gida a wasu kasashen Afrika, a cewar wata sanarwar ma'aikatar harkokin waje kasar Afrika ta Kudu (DIRCO).

Gwamnati da al'ummar Afrika ta Kudu suna allawadai da sace wadannan 'yan mata a cikin wata makaranta a tarayyar Najeriya da ake zargin kungiyar Boko Haram da aikatawa, tare da yin kira ga kungiyar da ta sake su cikin gaggawa, in ji mista Zuma a cikin wannan sanarwa.

Haka kuma ya jaddada cewa, gwamnatinsa na allawadai da duk wasu ayyukan ta'addanci, kuma ta'addanci abu ne da ba za'a iyar rufe ido kansa ba.

Shugaban Afrika ta Kudu ya bayyana cewa, ya kamata kungiyar AU ta dauki matakan gaggawa bisa babban matsayinta a nahiyar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro domin kawo karshen duk wasu kungiyoyin ta'addanci dake da hannu kan hare-haren dake shafar fararen hula. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China