Wata kotu a kasar Masar ta haramtawa 'yayan kungiyar Islama shiga takarar zaben shugaban kasa da majalisun dokoki na kasar, kamar dai yadda rahoton kamfanin dillancin labaru na kasar MENA ya bayyana.
Wata kungiya mai adawa da kungiyar Islamar ta Masar, mai suna "The Popular Front," ta shigar da kara kotu, inda ta nemi da a dakatar da musuluntar da kasar ta Masar. Wannan shigar da kara da aka yi ya haifar da yanke hukunci kotu, inda kotun ta umurci hukumar zabe ta kasar ta haramtawa 'yan takara daga bangaren kungiyar Islama ta Masar taka rawa a zaben da za'a yi.
Yanke hukuncin kotun, an yi shi ne makonni kadan kafin zaben shugaban kasar, wanda za'a yi a watan Mayu a karon farko, tun bayan da aka sauke tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi daga karagar mulkin kasar. (Suwaiba)