Babban bankin kasar Rwanda ya bayyana a ranar Litinin cewa, zai sanya wani sabon tsari domin kula da aike da kudi tsakanin bankunan kasar.
Shirin T24 Core Banking ya kunshe kyautata karfin gudanar ayyuka ga jama'a, kuma zai taimaka ga kyautata tsaro da sanya ido a harkokin cikin gida, saukaka daukar nauyin bayyanai cikin kankanin lokaci da kuma isar da bayanan tattalin arziki, in ji babban bankin Rwanda a cikin wata sanarwa.
Duk da an kawo wasu sauye-sauye a cikin 'yan shekarun baya bayan nan, amma a kalla 'yan kasar Rwanda miliyan 10,5 kawai suka shiga tsarin banki. Wannan karamin adadi na tada hankalin babban bankin da ya dauki nauyin kula da kafa wannan sabon tsarin. (Maman Ada)