Kasar Djibouti ta bayyana damuwarta tare da yin allawadai a ranar Laraba da tagwayen hare-hare da aka kai a wata kasuwar birnin Jos dake tsakiyar Najeriya a ranar Talata.
Bayan afkuwar wadannan munanan hare-hare, ma'aikatar harkokin wajen kasar Djibouti ta fitar da wata sanarwa, inda ta la'anci wadannan tagwayen hare-hare da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 118, tare da jikkata 56 a matsayin abin kunya da rashin imani.
Kasar Djibouti na aika ta'azziyarta ga iyalai da 'yan uwan wadanda hare-haren suka rutsa da su, da ma hukumomin kasar Najeriya, in ji wannan sanarwa.
A cikin wannan yanayi na tashin hankali, kasar Djibouti na kara jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Najeriya kan kokarin da take yi na yaki da ta'addanci. (Maman Ada)