Babban wakilin sakatare janar na MDD Sa'id Djinnit ya tatattauna da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Abuja game da batun 'yan matan nan da aka sace, da kuma rawar da majalisar ke takawa don taimaka wa wajen ganin an sake su.
Kakakin MDD Stepahne Dujarric ne ya bayyana hakan yayin taron majalisar da aka saba yi, inda ya ce, Mr. Ban ne ya bukaci Djinnit da ya yi tattaki zuwa kasar ta Najeriya don tattauna batun, kana ya gana da sauran jami'an kasar, tare da bayyana shirin majalisar na taimaka wa 'yan matan da iyayensu bayan an sake su.
Ya kuma sake nanata kudurin majalisar na taimaka wa gwamnatin Najeriya da dabarun yaki da ta'addanci kamar yadda dokokin MDD suka shimfida.
A cewar Dujarric, MDD ba ta da wasu kadadori a kasa ko ikon yaki da ayyukan ta'addanci a Najeriya. (Ibrahim)