in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira ga sabon yunkiri domin warware rikicin Saharawi
2014-04-17 09:59:59 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta yi kira da a kara rubanya kokari domin warware rikicin Saharawi.

Madam Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kwamitin kungiyar AU, ta yi maraba da sanarwar ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2014 bisa rahoton babban sakatare na MDD kan rikicin Saharawi, in ji tarayyar AU a ranar Laraba a cikin wata sanarwa.

Wannan rahoto ya kunshe jerin manyan batutuwa, wadanda suke hada da shawarwarin da aka kaddamar ta hanyar tura manzon musammun na sakatare janar na MDD domin tattaunawa tare da bangarori biyun masu gaba da juna, batun ayyakan tawagar MDD kan shirya zaben raba gardama a Saharawi (MINURSO) da kuma ayyukan jin kai da na kare hakkin 'dan adam, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China