in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta kammala shagulgulan cika shekaru 50 da bikin ranar Afirka
2014-05-26 09:48:03 cri

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta kammala shagulgulan cika shekaru 50 da kafuwar OAU da AU, da wani kasaitaccen biki da aka yi wa lakabin ranar Afirka.

Mataimakin shugabar hukumar ta AU Erastus Mwencha ne dai ya jagoranci bikin, wanda ya samu halartar manyan kusoshi, da wakilan kasashe mambobi, da ma'aikatan hukumar ta AU, tare kuma da ragowar baki da aka gayyata.

Bikin na ranar Lahadi wanda ya gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha dai, ya kunshi gabatar da jawabai da dama daga sassan masu ruwa da tsaki.

A sakonta game da shagulgulan da aka shafe shekara guda ana gudanarwa, shugabar hukumar gudanarwar kungiyar ta AU uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, cewa ta yi, bikin ya ba da damar bayyana kudurorin da ake fata nahiyar Afirka ta cimma na nan gaba.

Zuma ta ce, muradun da aka sanya gaba ya zuwa shekarar 2063, muradu ne masu dogon zango, wadanda kuma za su share fagen sauya akalar Afirka ya zuwa nahiya dunkulalliya, mai cike da zaman lafiya da ci gaba, wadda kuma za ta mai da hankali ga cimma bukatun al'ummarta.

Kafin wannan biki kuwa sai da aka gabatar da gudun yada kanin wani, da baje kolin nune-nunen tsarin aikin shige da fice na hadakar kasashe mabobin kungiyar. Duka dai a wani bangare na taya murnar nasarar da AUn ta cimma a shekaru 50 da suka gabata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China