Sabon firaministan Libiya Ahmed Maitiq, ya samu nasarar lashe kuri'ar amincewar majalissar dokokin kasar, wadda aka kada a jiya Lahadi, bayan zaben 'yan majalissar kasar mai cike da rudani, matakin da ya haifar da kafuwar gwamanatin 'yan ra'ayin Islama.
A cewar daya daga 'yan majalissar Mohammed Kilani, Maitiq ya lashe kuri'u 83 cikin 93 da aka kada yayin zaman na jiya. Bugu da kari, Kilani ya ce, gwamnatin sabon firaministan ta samu cikakken goyon bayan majalissar.
Kafin hakan dai, an zabi Maitiq a matsayin sabon firaministan kasar cikin watan Mayun da ya shude, sai dai wasu daga 'yan majalissar, ciki hadda mataimakin shugabanta Azzedine Awami sun kalubalanci sakamakon, bisa zargin karya dokar zabe.
Duk dai da nasarar da sabon firaministan ya samu a wannan lokaci, akwai tarin matsalolin da ka iya bijirowa, sakamakon rabuwar kai dake akwai tsakanin 'yan majalissa masu ra'ayin Islama da kuma 'yan baruwan mu. An ce, ko da a zaman na ranar Lahadi, 'yan majalissar dokokin kasar 93 cikin 200 suka halarci kuri'ar amincewa da sabon firaministan. (Saminu)