in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Libya ta yi kira da a karfafa matakan tsaro domin kare Tripoli
2014-05-20 14:20:15 cri

Shugaban majalisar dokokin kasar Libya ya ba da umurni ga sojojin sa kai dake goyon bayan gwamnatin kasar da su kiyaye tsaron Tripoli, babban birnin kasar, kwana guda bayan da wani gundun 'yan tawaye dake biyayya ga wani janar din soja ya kai hari kan ginin majalisar.

A cikin wata sanarwa zuwa "garkuwar Libya", wata kungiyar mayakan sa kai dake Misrata, shugaban kwamitin kasa, janar Nouri Abu Sahmain ya yi kira ga sojojin sa kan da suka tashi tsaye domin murkushe yunkurin da ake na yin juyin mulki kan birnin Tripoli.

Aikinku shi ne jibge mayakansu a Tripoli da kuma kare hanyoyin shiga da fita na birnin, har ma da manyan gine-ginen gwamnati da na hukumomin kasa da kasa, in ji mista Sahmain a cikin wata sanarwa.

Wani jami'in ofishin ministan tsaro da ya hiranta tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da ya bukaci a sakaya sunasa, ya tabbatar da cewa, mista Sahmain ya bukaci wannan taimako.

Kakakin kungiyar "Garkuwar Libya" Abu Bakar al-Enaira shi ma ya tabbatar da cewa, sun samu umurni domin kiyaye tsaro a kan muhimman hanyoyi da manyan gine-gine. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China