in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in sojan Libya ya bukaci da a wargaje majalisar dokokin kasar
2014-05-19 10:34:31 cri

Shugaban sojojin 'yan sanda na kasar Libya kanal Mukhtar Fernana, ya nemi da a sauke 'yan majalisar dokokin kasar, da kuma babbar majalisar hadin kan kasa, tare da kawar da 'yan ta'adda daga babban birnin kasar Tripoli.

Fernana wanda ya gabatar da sanarwa ta manema labarai, ya ce, jami'an sojojin kasar sun yanke shawara cewar, majalisar tsarin mulki ta kasar Libya ta maye gurbin 'yan majalisar kasar, to amma sanarwar ta amince wa firaministan kasar Abdullah Al-Thinni da ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulkin kasar, har sai an gudanar da sabon zaben kasa.

Wasu gungun 'yan tsagera a karkashin janar Khalifa Haftar mai ritaya, sun kai farmaki kan ginin 'yan majalisar dokokin kasar a ranar Lahadi, a inda suka kori 'yan majalisar, wannan ya sa tilas aka dage zaman majalisar da ake gudanarwa kafin isowar 'yan tsageran.

Sanarwar ma'aikatar lafiya ta Libya, ta ce, musayar wuta ta barke a kusa da ginin majalisar dokokin kasar, da kuma hanyoyi na zuwa da dawowa babban filin jirgin saman jiragen kasa da kasa na Tripoli, a inda kuma hakan ya haifar da asarar rayuka na mutane biyu, a inda kuma fiye da wasu mutane 60 suka jikkata.

Fernana dai ya ce, harin da aka kaiwa 'yan majalisar ba juyin mulki ba ne, amma wata hanya ce da ta dace da muradun juyin juya hali. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China