in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar wani abu a kasuwar Urumqin Sin ta haddasa mutuwar mutane
2014-05-22 10:47:11 cri

Rahotannin na nuna cewa, an samu yawan mutane da har yanzu ba a kayyade adadin su ba da suka mutu ko jikkata sakamakon fashewar wani abu a safiyar Alhamis din nan 22 ga wata a tsakiyar kasuwar Urumqi, babban birnin gundumar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Duk wadanda suka jikkata dai, an garzaya da su asibiti daban daban dake kusa, in ji wani jami'in 'yan sanda.

Wani da ya gane wa idanunsa ya bayyana cewar, wadansu manyan motocin safa guda biyu da suka fito daga arewaci zuwa kudancin birnin ne suka auka a kan mutane a cikin kasuwar da misalin karfe 8 saura minti goma na safiyar wannan rana, sannan suka wurga ababen fashewa ta ko ina daga cikin motocin. Ya ce, daya daga cikin motocin ita ma ta tarwatse, ta kama da wuta a cikin kasuwar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China