in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya sha alwashin aiwatar da hukunci mai tsanani kan maharani
2014-05-22 15:09:05 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha alwashin daukan mataki mai tsanani a kan maharani da suka kai mummunan hari a kasuwar Urumqi da safiyar Alhamis din nan, sannan kuma ya ce, zai yi duk abin da ya kamata na ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro.

Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a yau sakamakon harin ta'addancin da aka kai a kasuwar birnin Urumqi na gundumar Xinjiang mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Shugaba Xi ya kuma bukaci mahukuntar wannan yankin da su yi saurin aiwatar da bincike, sannan a samar wa wadanda suka jikkata jinyar da suke bukata, a kuma isar da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin.

Ya ce, gwamnatin kasar Sin za ta cigaba da aiki tukuru wajen yaki da ta'addanci, tare da kare lafiyar al'ummarta, harin da ya auku ta hanyar fashewar wadansu abubuwa a tsakiyar kasuwar Urumqi da safiyar yau din nan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 31, da wassu fiye da 90 da suka jikkata.

Wata tawaga karkashin jagorancin ministan tsaron al'ummar kasar Sin Guo Shengkun ya bar birnin Beijing da safiyar nan zuwa Urumqi domin tafiyar da ayyukan da suka shafi bincike da sakamakon da za'a samu da dai sauran su. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China