Rundunar 'yan sandan jihar Kano dake arewacin Najeriya, ta ce, wani harin bam da aka dana a jikin wata karamar mota ya hallaka mutane a kalla 5, tare da jikkata wasu mutane 4.
Harin wanda aka kaddamar a unguwar Sabon Gari mai yawan kiristoci ya faru ne da misalin karfe 9 da rabi na daren ranar Lahadi, a wani wuri dake da yawan zirga-zirgar jama'a.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kano Musa Majiya ne, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua aukuwar lamarin ta wayar tarho. Yana mai cewa, kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin dasa bam din.
Bugu da kari Majiya ya ce, tuni aka aike da jam'an tsaro da kuma 'yan sanda kwance bam domin nazaratar yanayin wurin da al'amarin ta wakana.
A hannu guda kuma wani mazaunin unguwar mai suna Ahmed Sambo, ya bayyanawa majiyar mu cewa, jim kadan da aukuwar lamarin jami'an tsaro sun yiwa yankin tsinke, ta yadda ba za a iya tantance me ke faruwa ba, ko da yake dai ya ce, a zaton sa fashewar ta hallaka mutane da dama.
Unguwa ta Sabon Gari dai ta gamu da makamantan wadannan hare-hare guda biyu a bara, wadanda bisa jimilla suka janyo salwantar rayukan mutane 100.
Hakan kuma na zuwa ne a lokacin da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram, ke dada kaimin kai hare-hare a sassan yankunan arewacin Najeriya daban daban. (Saminu)