in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guinea-Bissau za ta kara gudanar da zaben shugaban kasa a Mayu
2014-04-17 11:54:19 cri

Hukumar zabe ta kasar Guinea-Bissau za ta kara gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 18 ga watan Mayun wannan shekarar, domin yanke hukunci tsakanin 'yan takara guda biyu, masu neman kujerar shugabancin kasar, watau tsohon ministan kudi Jose Mario Vaz da kuma Nuno Gomes Nabiam, wanda ya tsaya takara a matsayin mai zaman kanshi, watau ba'a karkashin jam'iyya ba.

Hukumar zaben ta bayyana yanke shawarar kara gudanar da zaben a karo na biyu, bayan dukanin 'yan takarar sun kasa samun adadin kuri'un da ake bukata mafi rinjaye a zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a ranar 13, ga Aprilu shekarar da muke ciki.

A ranar Lahadin da ta shude ne kasar ta Guinea-Bissau ta gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan majalisun dokokin kasar. An gudanar da zaben ne tun bayan wani juyin mulkin dakarun sojojin kasar a shekara ta 2012, wanda ya haifar da koma bayan al'amurra a kasar, wacce ke Afrika ta yamma. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China