Gwamnatin kasar Norway ta alkawarta samar da tallafin kudi sama da dalar Amurka miliyan 1.67, domin kulawa da lafiyar kwakwalen yara 'yan mata 223 da 'yan Boko Haram suka sace a jihar Borno, tare kuma da karfafa tsaro a makarantun dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.
Ministan harkokin wajen kasar ta Norway Borge Brende ne ya bayyana hakan a jiya Talata, yayin ganawarsa da gungun 'yan kasar ta Norway masu rajin a saki 'yan matan.
Mr. Brende ya kara da cewa, ya damu kwarai da sace wadannan 'yan mata. Ya kuma yi tir da yadda kungiyar ta Boko Haram ke kokarin mai da yaran 'yan makaranta tamkar wata ganimar yaki. (Saminu)