in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka na taimaka wa Nigeriya neman 'yan matan da aka sace
2014-05-06 10:01:48 cri

Amurka ta sanar da cewa, tana taimaka wa Nigeriya wajen neman 'yan makarantan nan 'yan mata su fiye da 200 da kungiyar 'yan ta'addan nan ta Boko Haram suka sace.

Jay Carney, kakakin fadar White House a bayanin da ya yi wa manema labarai Litinin din nan ya ce, taimakon da kasar ke bayarwa ya dogara ne bisa ga bayanai da take musanyawa tsakanin ta da Nigeriya tare da inganta harkokin binciken kimiyya na tantance 'dan adam da fadada karfin binciken, domin a cewar ta, Amurka na kallon abin da ya faru a matsayin abin takaici, kuma mummunan tashin hankali.

Jay Carney ya ce, an riga an yiwa shugaba Obama bayanin sau da dama game da halin da ake ciki dangane da 'yan matan da aka sace, kuma hukumar tsaron kasar tana sa ido sosai akan wannan lamari.

Fiye da 'yan makaranta 200 na makarantar 'yan mata dake garin Chibok a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriya da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram suka sace a watan jiya, abin da kungiyar ta dauki alhakin aikatawa a Litinin din nan tare da barazanar sai da su. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China