Cikin dalilan da aka lissafa da suka kawo wannan fashewar bututu, akwai shimfida bututun mai ba yadda ya kamata ba tare da bututun ruwa na gidajen jama'a, sakaci da aikin duba wadannan bututu a kai a kai da kuma saka wadanda ba kwararru ba su duba yoyon da bututun ke yi kafin ya kai ga fashewa, in ji Yang Dongliang wanda shi ne shugaban hukumar kula da gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali ta kasar Sin.
Mr. Yang ya bayyana hakan ne a birnin Qingdao a lokacin rangadin aiki da aka yi da kwararru masu binciken yadda wannan hadari ya abku, wanda ya yi sanadiyar rasuwar mutane 55, 136 kuma aka kai su asibiti sannan har yanzu mutane 9 sun bace ana neman su.(Fatimah)