in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira da aka saka matan Afrika cikin harkokin kudi
2014-05-22 10:40:24 cri

Jami'an gwamnati da masu fafutukan 'yanci mata a taron da yanzu haka ake gudanarwa na bankin cigaban Afrika ADB a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, sun bukaci gwamnatoci su 'yanta mata ta hanyar saka su cikin ayyukan tattalin arzikin nahiyar domin a samu cigaba mai karko.

Da suke magana a wani zama na musamman a kan daidaiton jinsi a ranar Laraban nan 21 ga wata, sun yi kira da a yi adalci da kuma aiwatar da komai a bayyane wajen samar da filaye, bayar da rancen kudi, da kuma ilimi ga mata a duk inda suke a nahiyar Afrika.

A jawabinta, Ngazi Okonjo-Iweala, ministar kudin Nigeriya ta ce, cigaban da ake samu a nahiyar da suka hada da kasar Nigeriya yana da daraja, sai dai bai iya magance banbancin jinsi da ake fuskanta ba, a don haka sai ta yi kira da a kara tattauna yadda za'a saka mata a hanyoyin tattalin arziki domin cigaba.

Ta jaddada muhimmancin inganta ilimin 'ya'ya mata da 'yantar da su a bangaren tattalin arziki domin a rage banbancin da ake fuskanta na jinsi a nahiyar. Ta ce, yanzu haka saka yara mata a makarantu a Nigeriya ya kai kashi 40 a cikin 100 a jihar Kano dake arewacin kasar, inda aka bullo da wani tsari na baiwa iyaye wassu adadin kudi ga duk wanda ya kai 'yarsa makaranta.

Sai dai an lura da cewa, kai yara makaranta ba kawai yana ba su ilimin da ya kamata ba ne wajen shiga a dama da su a tattalin arzikin kasashensu, har ma yana rage matsalolin da ake fuskanta, dalilin aurar da yara kanana da suka hada lalurorin da suke samu lokacin haihuwan, in ji shugaban ofishin mata na MDD Phumzile Mlambo-Ngcuka wadda ta lura da cewa, aurar da yara da wuri shi ke kara kawo banbancin jinsi da ake nunawa.

Ta ce, ganin yadda mata ke taka rawa wajen samar da manyan kayayyakin tattalin arziki a bangaren ayyukan noma a Afrika, sannan kuma a ce adadin su dan kadan ne ke da 'yancin mallakan filaye, akwai bukatar baiwa mata karin dama ga abubuwan da ake amfani da su a fannin noma. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China