in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mutane 5 a harin da aka kai a arewacin Najeriya
2014-05-14 10:52:06 cri

Jami'an 'yan sanda a jihar Taraba, dake arewa maso gabashin kasar Najeirya sun tabbatar da cewar, mutane 5 sun mutu a Kugwana dake yankin karamar hukumar Bali, a sakamakon wani hari da wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba, suka kai a yankin a safiyar Talata.

Kakakin 'yan sandan jihar Taraba, Joseph Kwali ya shaidawa manema labarai a birnin Jalingo, babban birnin jihar ta Taraba cewar, wadansu Fulani da ake zargi su ne suka kai harin, tare da jikkata wasu mutane biyu, sun kai harin ne a kan kauyen da misalin karfe 2 na dare, agogon Najeriya.

Kakakin 'yan sandan ya ce, tuni rundunar 'yan sandan ta tura da jami'an tsaronta zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

Kabilun Jukun da na Tiv da Fulani dake karamar hukumar tuni ne suka sanya hannu a kan wata yarjejeniyar samar da zaman lafiya, a ranar 29 ga watan Aprilu, a kokarin da aka yi na dakatar da fadace-fadace da juna, wanda yin hakan ya rarraba kawunan kabilun, fiye da tsawon shekara guda.

Shi dai wannan rikicin a bangaren dake cikin jihar ta Taraba ya haifar da asarar rayukan jama'a da dama, tare da yin sanadiyyar asara ta dukiyoyi. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China