Wani bam da aka dana cikin wata karamar mota ya tarwatse a unguwar Sabon Gari dake Kano a arewacin Najeriya. Lamarin da ake kyautata zaton ya janyo asarar rayuka da dukiya mai yawa.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kano Musa Majiya, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua aukuwar lamarin ta wayar tarho. Inda ya ce, harin da ya auku a daren ranar Lahadi, a wani wuri kan titi dake unguwar ta Sabon Gari ya haifar da babbar kara, ko da yake a cewar sa, ba a kai ga tantance yawan wadanda fashewar ta ritsa da su ba.
Bugu da kari Majiya ya ce, tuni aka aike da jam'an tsaro da kuma 'yan sanda kwance bam domin nazartar yanayin wurin da al'amarin ta wakana.
A hannu guda kuma wani mazaunin unguwar mai suna Ahmed Sambo, ya bayyana wa majiyar mu cewa, jim kadan da aukuwar lamarin, jami'an tsaro sun yi wa yankin tsinke, ta yadda ba za a iya tantance me ke faruwa ba, ko da yake dai ya ce, a zatonsa, fashewar ta hallaka mutane da dama.
Unguwa ta Sabon Gari dai ta gamu da makamantan wadannan hare-hare a baya, wadanda bisa jimilla suka janyo salwantar rayukan mutane 100.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, sai dai sau da dama kungiyar nan ta 'yan kaifin kishin Islama da ake kira Boko Haram, ta sha kai makamantan wadannan hare-hare a sassan yankunan arewacin Najeriya daban daban. (Saminu)