in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu za ta kara mai da hankali ga diplomasiyyar Afirka
2014-05-15 10:20:15 cri

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu, ya ce, kasarsa za ta kara mai da hankali kwarai ga bunkasa diplomasiyyarta da kasashen nahiyar Afirka.

Hakan a cewar sa na da alaka da tarihin yadda kasar ta samu kubuta daga kangin wariyar launin fata karkashin jam'iyyar ANC mai mulki.

Shugaban Zuma wanda ya bayyana hakan yayin da yake karbar takardun karrama kasarsa daga manyan jami'an diplomasiyyar ta jiya a birnin Pretoria, ya kara da cewa, matsayin kasarsa a yanzu zai ba ta damar fuskantar kalubalen sauya alkiblar nahiyar, ta yadda za a kai ga bunkasa tattalin arzikinta, tare da burin dunkulewar ta wuri guda.

Har ila yau Zuma ya ce, tuni Afirka ta Kudu ta taka rawar gani, wajen inganta samar da ababen more rayuwa a nahiyar, karkashin shirin samar da ci gaba na hadin gwiwa na (NEPAD), da kuma shirin fadar gwamnatinsa na inganta samar da ababen more rayuwa da aka kaddamar cikin watan Yulin shekarar 2010.

Kaza lika shugaban ya ce, kasar tasa za ta dora kan ayyukanta na tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya, da magance rigingimu, da yaki da fatara da dai sauran su. Za kuma ta kara himma wajen ganin yankin kudancin Afirka ya samu ci gaban da ake fata karkashin kungiyar SADC, wadda ke aiki kafada-da-kafada da takwararta ta AU.

Ya zuwa shekarar 2012 da ta gabata dai, ofisoshin jakadancin kasashen waje dake Afirka ta Kudu sun kai 315, wanda ya kasance matsayi na biyu a duk duniya bayan birnin Washington na Amurka. Bugu da kari ofisoshin jakadancin kasar na waje sun karu daga 34 a shekarar 1994, zuwa 126 a shekarar ta 2012. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China