Sabon firaministan kasar Libya, Ahmed Maitiq ya bayyana cewar, yana da niyyar kafa majalisar gudanarwa da za ta tunkari rikicin da ake yi a kasar a yanzu.
A cikin wani jawabin da ya yi wanda aka nuna ta kafofi gidan talabijin, Maitiq ya ce, a halin da ake ciki yana ganawa da mutane daga dukannin jam'iyyun kasar, domin kafa gwamnatin da za ta fuskanci halin kalubale da kasa ke ciki, tare da daidaita jama'ar kasar ta hanyar kafa majalisar dokokin kasar.
Maitiq ya ce, sabuwar majalisar dokokin kasar za ta karfafa ikon gwamnati da samar da 'yancin yan kasa, tare da kara habbaka harkar tsaro, da kuma hukumomi na soji, domin tunkarar halin ko ta kwana da ake ciki a yanzu.
Wasu kwararru sun yi hasashen cewar, ta yiwu sabon firaministan ya nada wasu ministoci a muhimman wurare, domin samar da karamar majalisar gudanarwa wacce za ta fara aiki, kuma a gefe guda, gwamnati za ta dinga gudanar da yarjejeniya da kungiyoyi daban daban a kan sauran mukaman gwamnati. (Suwaiba)