in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya na cigaba da bincike a Abuja bayan harin tashar motoci
2014-04-24 09:51:48 cri

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi kiran mazaunan birnin Abuja da kewaye da su ba da hadin kai game da kai da kawon motoci kan hanyar dake tashi daga Nyanya zuwa Abuja, inda ta bayyana cewa, ana fatan ba za a kawo jinkiri ba ne ga motoci. A cikin wata sanarwa, janar Chris Olukolade, kakakin hedkwatar tsaron kasar ya bayyana cewa, yawan cinkoson da ake samu kan hanyar na da nasaba da binciken da ake yi wa motocin dake shiga tsakiyar birnin Abuja.

Haka ya bayyana cewa, masu bin wannan hanya, da ma mazauna birnin sun nuna damuwarsu kan wannan matsala.

A cewar kakakin rundunar sojojin Najeriya, wadannan ayyuka sun wajabta, dalilin barazanar tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Kasar Najeriya ta zama dandalin hare-hare a wannan mako, inda bom ta tashi a wata tashar mota dake birnin Abuja a ranar Litinin da ta gabata, tare da haddasa mutuwar mutane 75. Daga baya kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai kazamin harin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China