Akalla an tabbatar da kashe mutane kusan 20, a wadansu hare-hare da wasu 'yan bindiga suka kaddamar, a kan wadansu kauyuka guda biyu dake cikin Nigeriya a ranar Laraba, kamar dai yadda kafofin yada labarai suka ruwaito bahasin jami'an tsaro da kuma wadanda aka yi abin akan idanun su.
Wata jarida da ake bugawa a kafar sadarwa ta Internet, mai suna 'Premium Time" ta ce, a safiyar jiya Laraba ne wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba, suka kai hari a kan kauye Wala, wanda ke da nisan kilomita 130 daga babban birnin jihar, Maiduguri, dake arewa maso gabashin Nigeriya, a inda bude wutar 'yan bindigar ya haddasa mutuwar mutane, wadanda adadin su, ba su kasa sha takwas ba.
Hakazalika, Majiyar jami'an tsaro, ta ce, wasu 'yan bindiga sun kai hari a kan kauyen Sabon-Kasuwa, wanda ke karamar hukumar Hawul dake cikin jihar ta Borno, inda barin wutar da suka yi ya tada hankulan jama'a.
Ita ma karamar hukumar Gwoza, wacce ke kan iyaka da Kamaru daga kudanci, sannan kuma daga arewacinta na iyaka da dajin Sambisa mai yawan manyan tsaunuka, inda kuma nan ne mabuyar mayakan 'yan kungiyar Boko Haram, ta sha fuskantar muggan hare-hare a kwanan nan. Yanki dai yana kilomita 130, daga karamar hukumar Chibok, inda a nan ne wasu mutane da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sace yara yan mata fiye da dari a ranar Litinin din da ta gabata. (Suwaiba)