in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana muhimman kayayyakin more rayuwa a matsayin kafar samun ci gaba mai dorewa
2014-02-19 10:03:27 cri

Shugaban babban zauren MDD na wannan karo John W. Ashe, ya yi kira ga kasashe mambobin majalisar, da su bullo da nagartattun manufofi da dabarun warware matsalolin ruwan sha, tsaftar muhalli da makamashi mai dorewa, muhimman abubuwan da aka bayyana a matsayin kalubale ga ci gaban duniya.

Jami'in ya bayyana ne, yayin jerin muhawarar zaunen majalisar na farko da zai jagoranta a wannan shekara, don nusar da mambobin kasashe da sauran masu ruwa da tsaki, ta yadda za su kimtsa game da ajandar bunkasuwa bayan shekarar 2015.

Ya ce, yanzu haka akwai mutane miliyan 783 da ba su da ruwan sha mai tsafta, yayin da mutane biliyan 2.5 ke zaune a wuraren da babu tsaftar muhalli, kana wasu mutane biliyan 1.4 ba su da hasken wutar lantarki.

Mr. Ashe ya ce, muddin ana bukatar cimma manufofin muradun karni na MDD, tare da samun ci gaba, wajibi ne a magance matsalar muhimman kayayyakin more rayuwa, wadanda suka kasance ma'aunin kimanta talauci, harkar lafiya, bambancin jinsi tsakanin al'umma da sauransu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China