Kimanin masu hakar ma'adinai fiye de goma ne kasa ta rufta da su a cikin rugujewar wata mahakar ma'adinai ba bisa doka ba dake arewacin kasar Mozambique, inda a kalla mutane biyar suka mutu zuwa wannan rana, in ji gidan talabijin na STV.
Hadarin da ake ganin shi ne mafi muni da aka taba samu a arewacin kasar, ya faru a ranar Litinin da yamma a cikin watan mahakar ba bisa doka ba dake yankin Memba, a cikin gundumar Namputa, inda mutane fiye da goma, da yawancinsu matasa, suka aiki, in ji STV. Har yanzu ba'a da masaniya kan zinari suke nema ko wasu karafe masu daraja. A cewar kamfanin dillancin labarai na AIM da ya rawaito wata majiya ya bayyana cewa, kusan mutane talatin ake zaton kasa ta rufe da su. (Maman Ada)