in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu da Britaniya sun aikawa Nigeriya sakon ta'aziyyar fashewar bam
2014-04-15 10:58:54 cri

Afrika ta Kudu ta aike da sakon ta'aziyyarta na nuna alhinin ga Nigeriya, a sakamakon harin bam din da aka kai babban birnin kasar Abuja, wanda ya haddasa asarar rayuka sama da 70.

Wata sanarwa wacce ta fito daga sashen hulda da kasashen waje, ta kasar ta Afrika ta Kudu ta ce, Afrika ta Kudu ta yi amanna cewar, ko wace sigar ta'addanci daga ko'ina ba wani abu ba ne da za'a lamunta da shi ba.

Hakazalika sakataren harkokin wajen Britaniya William Hague, shi ma ya yi Allah wadai da wannan hari da aka kai a babban birnin kasar ta Nigeriya, a inda ya jaddada karin goyon bayan Britaniya ga kasar, wacce ke nahiyar Afrika.

Sanarwar sakatare harkokin wajen Britaniyar ta fito daga ofishin harkokin wajen Britaniya da kuma ofishin kasashe renon Ingila a jiya Litinin.

Hague ya ce, Britaniya za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da gwamnatin Nigeriya, domin taimaka mata wajen magance barazanar da take fuskanta ta ta'addanci. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China